Tuesday, 27 November 2018

PHP Tags-PHP 2

PHP TAGS
PHP script php script yana farawa da  <?php sannan kuma yana karewa da ?>:
misali:
<?php
// PHP anan ne za asa php code.
?>
a kula a php akwai abun da ake kira da comment wanda kowanne programming language yana da salon da akeyinsa,anfanin comment shine ko karubuta abu to bazaiyi anfaniba indai acikin comment ne,kawai anayinsa ne dan alama.
Ana anfani da // slash guda biyu wajen yin comment a php,
misali:
//wannan comment ne.
Yanda Ake Rubuta PHP
ga misalin yanda ake rubuta PHP nan  a kasa wanda output dinsa shine "Barka".

<html>
<head>
<title>Shafin PHP na nafarko</title>
</head>
<body>
<?php
echo "Barka!";
?>

</body>
</html>
duk wani statement na php yana karewa ne da  semicolons (;)

Gabatarwa Kan PHP-PHP 1

PHP dai kamar yanda muka sani wani yare ne da ake anfani dashi kyauta wajen hada shafukan yanar gizo,yana daga cikin manyan yarukan programming a duniya.Ana executing ko kuma running na PHP script acikin server(computer ko kuma internet).
daga cikin manyan shafukan da aka gina su da PHP akwai wordpress da kuma facebook.
Abubuwan da PHP ke iyayi:
-Kirkarar motsattsen(dynamic) shafin yanar gizo(web page)
-Kirkira,budewa,rufewa,rubutawa da kuma goge files acikin server.
-Sanyawa da chanzawa da gyara abubuwa acikin rumbun adana bayanai(database).
-dasauransu.